<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>195</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Mai fansarmu, da za ya hau ya bar mai taimako
 Ya bi da mu, ya zauna kuwa a cikinmu.

[V2]
 2) Shugabanmu, mai bayarwa, da yardar rai ya zo,
 Ya hura mana ƙaunarsa a zuciyarmu.

[V3]
 3) Ya. zo da kamar kurciya, shaidar salama shi,
 Da nufin ba da lafiya ga duniya duko

[V4]
 4) Tasa kuwa wannan murya a zuciya mu kan ji,
 Mai tsautawa, mai ta'aziyya, mai ƙauna kuwa.

[V5]
 5) Idan fa mun yi nasara, idan da tsabtar rai,
 Ko tunani mai tsarki, shi ne ya bayar.

[V6]
 6) Ya Ruhun Tsarki, Ruhun Rai, bayyana ikonka,
 Ka kau da rashin ƙarfinmu, ka cika mu.</lyrics>
<title>Mai Fansarmu, da Za Ya Hau Ya Bar Mai Taimako LW195</title>
</song>